Barcelona ta raba maki a gidan Getafe a La LigaGetafe Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Getafe da Barcelona sun tashi 0-0 a wasan mako na 29 a gasar La Liga ranar Lahadi da suka kara a filin wasa na Coliseum Alfonso Perez.

Karo na hudu da kungiyar Camp Nou ta raba maki a gasar La Liga ta kakar nan, bayan fafatawa 29 da aka yi a gasar.

Barcelona ta ci karawa 23 a La Liga da canjaras hudu aka doke ta wasa biyu.

Kungiyar da Xavi ke jan ragama ta ci kwallo 53 aka zura mata tara, mai maki 73.Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like