Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Karu Da Fiye Da Kaso 50 Cikin Dari A Shekaru 2Ofishin da ke kula da basussukan da ake bin Nijeriya DMO ya bayyana cewa adadin basussukan sun karu da Naira Tiliyan 7.1 a cikin shekaru 2.

Alkaluma sun bayyana cewa watanni biyu kafin hawan shugaba Buhari karagar mulki, basukan sun tsaya akan Naira tiriliyan 12.06, amma yanzu sun kai Naira tiliyan 19.16.

Basussukan gwamnatin tarayya na cikin gida sun kai Naira tiriliyan 11.07, inda suka karu da kaso 40.71 cikin dari daga adadin su na Naira tiriliyan 8.51 a watan Maris na 2105.

Basukan da ake bin kasar daga waje kuwa (na gwamnatin tarayya da na jahohi) ya karu daga Dala biliyan 9.46 zuwa dala biliyan 13.81. 

Wannan ya nuna cewa an samu karin kaso 45.98 cikin dari.

DMO ya bayyana cewa an kiyasce adadin bashi wannan shekara ne akan farashin canjin N306.35 akan kowacce Naira, yayin da aka kiyasce adadin bashin shekarar 2015 akan N197 akan kowacce Naira, wanda shi ne farashin canji na wannan lokaci.

You may also like