Batun Sakin ‘Yan Matan Chibok Frofaganda ne – Fayose


 

 

Gwamnan jahar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana cewa batun sakin ‘yan matan Chibok zai iya kasancewa wata frofaganda ta gwamnatin Buhari domin ta karkatar da hankalin mutane daga mawuyacin halin da kasar ke ciki.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya ta hannun mai bashi shawara akan harkokin yada labarai, Lere Olayinka, gwamnan ya bayyanan cewa wannan al’amari abun duba ne domin kuwa halin jam’iyyar APC ne ta karkatar da hankalin mutane a duk lokacin da ta kwafsa, inda ya yi tuni akan kama alkalai da gwamnatin Buharin ta yi a makon da ya gabata.

Gwamnan ya kuma ce ‘yan Nijeriya a yanzu sun gaji da karairayi da yaudarar gwamnatin APC, ya kara da cewa abun da kasar ke bukata shi ne a bunkasa tattalin arzikin ta mutane su samu abinci.

Ya yi tuni game da lokacin da aka ce daya daga cikin ‘yan matan Chibok din ta kubuta, wanda ya ce daga bisani aka gano ko turanci bata iya ba.

Sannan gwamnan ya janyo hankalin mutane game da harin Bomb din da ‘yan Boko Haram din suka kai kwanaki biyu da suka wuce.

Ya kara da cewa shi dai bai yarda ba da wannan al’amari, kuma ‘yan Nijeriya ma kar su yanke hukunci tukunna sai sun ga matan da idanunsu.

A karshe ya ce “frofaganda, karya da yaudara dole su kau ta yadda za’a samu gwamnati ta gari a Nijeriya”

You may also like