Batun shigar Ukraine cikin NATO da saura | Labarai | DWShugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine, ya yi kira ga kungiyar tsaro ta NATO da ta bude wa kasar kofar zama mamba a cikinta, a taronta na gaba da za a yi a cikin watan Yulin wannan shekara.

Shugaban na Ukraine ya yi kiran ne lokacin da Sakatare na kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya ziyarci kasar a karon farko tun bayan mamayar Rasha.

Mr. Stoltenberg din ya ce Ukraine na da damar shiga kungiyar, kuma batun tsaronta zai kasance cikin jerin manyan batutuwan da taron NATO na gaba zai mai da hankali a kai.

Sai dai kuma da yammacin jiya Alhamis ne ministan tsaron Jamus Boris Pistorius, ba a wannan lokaci ne ya kamata Ukraine ta shiga cikin kungiyar ta kawancen kasashen yammacin duniya ba.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like