Batun ‘yan gudun hijira ya mamaye taron duniya


 

 

A ranar Litinin din nan ce aka bude taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 71 a birnin New York na Amirka, inda kuma ajandar taron a karon farko ta mai da hankalin kan batun ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani.

USA Gipfel zu Flüchtlingen und Einwanderer der UNBan Ki-moon daga hagu, Peter Thomson shugaban taron karo 71 da Mogens Lykketoft shugaban taron karo na 70

Da yake bude babban taron na Majalisar Dinkin Duniya Mogens Lykketofts shugaban taron karo na 70 ya ce al’umma a duniya da ke fuskantar rikice-rikicen yaki da matsin tattalin arziki sun kai sama da miliyan 65, hakan ya tilasta kwararar ‘yan gudun hijira wanda ba’a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu zuwa kasashen duniya daban-daban musamman masu arziki don neman mafaka, muna fata wannan taro zai samar da mafita ga batutuwan da muka amince mu tattauna.

Griechenland Ankunft Syrische FlüchtlingeDubban mutane ke zama ‘yan gudun hijira saboda bala’oi a kasashensu

Ana dai fatan ganin shugabannin kasashen duniya za su samar da wani daftari kan batun ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani da zummar samar da kyakkyawar makomarsu, da kuma kawo karshen rikicin kasar Siriya.

Gwamantocin kasashen duniya da ke halartar taron suna da ra’ayoyi mabanbanta kuma mafi akasari sun ki amincewa da tsarin daukar nauyin ‘yan gudun hijira, to amma Mista Ban Ki-moon ya jaddada bukatar yin hakan da kuma kiran a samar da tsarin tsugunar da ‘yan gudun hijirar, kamar yadda yake jawabi a taron:

USA UN-Gipfel zum Thema Flucht und Migration in New York - Ban Ki MoonBan Ki-moon na son ganin an kawar da matsalar kwarar ‘yan gudun hijira.

“Dukkan kudurin da zamu cimma a yau dole mu hada gwiwa da aiki tukuru da kare hakkin ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani ba tare da nuna banbanci ba. Ina kira ga kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su kara yawan tallafi ga kasashen da suke fuskantar tashin hankali”.

To sai dai Kungiyar Amnesty International ta baiyana taron da cewa an yi sake babbar dama ta kubuce na samar da ingantaccen jadawali na duniya domin shawo kan matsalar, yayin da a nata bangaren Kungiyar Human Rights Watch ta ce shugabannin duniya ba su nuna kudiri mai karfi ba kan batun ‘yan gudun hijira masu neman mafaka.

You may also like