Batutuwan Da Majalissar Ministoci Ta Amince Dasu A zamanta na yau. 


A zaman da majalisar ministoci ta yi a yau Laraba a karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari ta amince da kammala aikin samar da wutar lantarki ta hanyar iska wanda aka yi watsi da shi a Katsina tun a shekarar 2012.
Da yake bayani a bayan taron, Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola ya ce, majalisar ta amince da kashe Naira milyan 700 don kammala aikin ginin sakatariyoyin ma’aikatan gwamnatin tarayya da aka tura jihohin Gombe, Nasarawa, Bayelsa, Osun, Anambra da kuma Zamfara.
Ya kara da cewa majalisar ta kuma amince da samar da tashar ta ruwa ta Harkokin masana’antu a Badagry da ke jihar Legas sai kuma batun mayar da wata fasahar horas da matuka jirgin sama daga Legas zuwa kwalejin koyar da tukin jirgin sama da ke Zaria wanda shi ma majalisar ta amince da yin haka a zamanta na yau.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like