Kwanaki kadan bayan wasu yan majalisa sun yi barazanar tsige shi, shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar Asabar ya hada fuska da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma na majalisar wakilai Yakubu Dogara.
Mutanen uku sun hadu ne a wajen taron walimar bikin yar gidan sakataren gwamnatin tarayya, Boss Musapha da aka yi babban dakin taro dake fadar shugaban kasa.
Wannan ce haduwarsu ta farko da shugaban kasar bayan da wasu yan majalisar suka bijiro da batun tsige shi kan kashe kudi da ya yi daga asusun rarar mai ba bisa ka’ida ba.
Shugaban ya amince a kashe kudin har dalar Amurika miliyan $496 domin sayo jiragen yaki daga kasar Amurka.
A makon da ya gabata yan majalisar sun soma yunkurin fara tsige shugaban kasar kan bada umarnin fitar da kudin sayen jiragen da ya yi ba tare da yan majalisar sun saka kudin a cikin kasafin kudi.
Sauran mutanen da suka halarci taron sun hada da jagoran jam’iyar APC na kasa Bola Ahmad Tinubu, da kuma gwamnonin jihohin Adamawa Kaduna, da kuma Ogun.