Bayan kwanaki 13 masu garkuwa da mutane sun sako mata, ‘ya’ya da yan uwan kwamishinan matasa na jihar Zamfara


Yaya, yan uwa da kuma matar kwamishinan matasa na jihar Zamfara da aka yi garkuwa da su kwanaki 13 da suka wuce sun samu yancin kansu.

Kenneth Ebrimson, kwamishinan yan sandan na jihar shine ya bayyana haka a Gusau babban birnin jihar.

“Ina farin cikin sanar daku cewa da yammacin yau mata da yaya da kuma yan uwan kwamishinan matasa da wasanni, Alhaji Abdullahi Gurbin- Bore wadanda aka yi garkuwa da su sun samu yancinsu,”ya ce.

“Ko kwabo ba a biya masu garkuwar ba kafin a sako su inda ya ce an sake su ne sakamakon matsin yan sandan da kuma sauran jami’an tsaro da masu garkuwar suka fuskanta.”

Gurbin-bore ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su sun koma gida.

Kwamishinan yan sandan ya koka kan karin mutanen da ake samu wadanda ke sanar da bata gari bayanai.

You may also like