Bayan shekaru 34: Gwamnatin Masari Ta Farfado Da Kamfanin Kusa Na Kankiya


 

Harkokin tattalin arziki abubuwa ne da suka dogara da abubuwa daban-daban. Haka kuma bunkasasu na bukatar daukar matakai dabandaban.

Wannan ya sa Hukumomi ko gwamnatoci kan  nazarci yanayin da suke ciki, da abubuwan da suke bukata domin samar da kyakkyawan yanayin da za su habaka hanyoyin tattalin arzikin da za su inganta rayuwar jama’ar jiharsu, kasa da sauran duniya.

Wannan ya sanya gwamnatin jihar Katsina, a karkashin jagorancin Mai girma Dallatun Katsina, Hon. Aminu Bello Masari ta yanke shawarar gudanar da taron tattalin arziki da zuba jari a harkokin Jihar Katsina domin ta bayyana wa duniya irin albarkar da Allah ya jibge a cikin jihar, wadanda in aka zakulo su, kuma aka sarrafa su za su samar da arziki mai dimbin yawa, ta yadda za a yi bankwana da talauci da rashin kwanciyar hankali ba tare da kyashin juna ba.

Daya daga cikin abubuwan da aka gano a yayin wancan taro, shi ne a farfado da masana’antun da ake da su, tare da kafa sabbi domin biyan bukatu biyu ko uku. Da farko akwai hana ci gaba da hasarar da ake yi a jarin da aka zuba cikin irin wadancan masana’antu. Sannan akwai batun samar da irin kayan da irin wadannan masana’antu ke samar wa domin biyan bukatun jama’ar jihar a kai tsaye ko a kaikaice.

Abu na uku shi ne, farfado da wadannan masana’antu zai samar da aikin yi ga dimbin mutane, musamman matasa masu jini a jika, wadanda suke da zimmar yin amfani da wannan karfi da basirar da Allah ya ba su domin biyan bukatun rayuwarsu.

Wadannan masana’antu sun hada da kamfanin kusa na Kankiya da ke Karamar Hukumar Kankiya. Shi wannan kamfani yana cikin tsoffin kamfanonin da gwamnatin Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ta kafa a 1982 a tsohuwar jihar Kaduna. Domin cimma wannan buri, gwamnatin Jihar Kaduna ta wancan lokacin ta kulla yarjejeniyar gudanar da wannan kamfani da kamfanin Sarrafa karfe da kusoshi da ke Lagos a 1983.

Sai dai tun daga wancan lokacin, kamfanin ya gaza mikewa. Hasali ma in ba domin gine-ginen kamfanin ba, ana iya cewa babu wani abin da ke akwai a cikinsa har ya zuwa shekarar 2001. A tsakanin 2001 da 2003, gwamnatin jihar Katsina a karkashin Marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa, an yi kokarin farfado da wannan kamfani, domin har an samar da dukkan injuna da kayan da wannan kamfani ke bukata, kuma aka gwada wadannan kaya, tare da tabbatar da suna aiki yadda ake bukata a watan Nuwamban 2003. Daga nan kuma batun kamfanin ya bace.

Amma saboda burin da gwamnatin Jihar Katsina ke da shi domin bunkasa harkokin masana’antu a jihar, sai aka kafa kwamiti domin sayar da duk irin wadannan kamfanoni ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu. Wannan kwamiti ya kasance a karkashin Marigayi Alhaji Garba Ja Abdulkadir.
Daga cikin shawarwarin da kwamitin ya gabatar, akwai zuba jarin Naira miliyan 77.5, inda gwamnatin jiha za ta samar da Naira Miliyan 67, Kananan Hukumomi su samar da jarin Naira Miliyan 8.5, yayin da KIPDECO zai samar da Naira Miliyan 1.2.

A cikin wannan yanayi negwamnatin Alhaji Aminu Masari ta sami wannan kamfani da sauran irinsa da ke cikin jihar Katsina. Domin ci gaba da daukar matakan farfado da wannan kamfani, gwamnatin Masari ta samar da Naira Miliyan biyar domin farfado da ayyukan kamfanin a 2015.
Sakamakon taron tattalin arziki da zuba jari da gwamnatin Masari ta gudanar a watan Mayun 2016, kamfanin Ampri Global Limited ya nuna sha’awa a harkokin kamfanin kusar na Kankiya. Inda bayan nazarin kamfanin da kuma hangen mafita, ya san Ampri Global Limited ya amince ya shiga cikin harkokin kamfanin.

Bayan mulmula kusoshi iri-iri, wadanda za su rika jawo masu hada-hadar harkokin da suke da alaka da kusa, kamfanin Ampri Global Limited zai rika harhada kekunan hawa da Keke NAPEP  da bututun ruwa domin biyan bukatun jama’a na kusa da na nesa
Haka kuma kamfanini ya sha alwashin kafa masakar tufafin sojojin sama da sauran Hukumomin da ke da alaka da tsaro a Malumfashi.

Haka kuma kamfanin ya bayyana cewa yana mu’amala da harkokin kiwon kifi, wanda zai jawo hankalin masu sana’ar kifi daga ciki da wajen jihar Katsina. Wannan babban al’amari ne a harkokin bunkasa rayuwar jama’ar jihar, musamman yankunan da aka kafa irin wadannan masana’antu da karuwar arziki a cikin jihar da kuma Nijeriya baki daya.
Bayan haka, wannan mataki zai haifar da guraben aiki ga mutane da yawa, tare da magance daya daga cikin manyan matsalolin da gwamnatin Masari ke kai gwauro tana kai mari domin magancewa. Haka kuma wannan al’amari zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro saboda matasa, majiya karfi da suke zaman kashe wando, wadanda ke barazana ga harkokin tsaro, za su samu tagomashin rayuwa, su kauce wa duk wadansu halaye, ko al’adun da za su jefa su cikin halaka.
Rahotanni na nuna cewa wannan kamfani zai samar da ayyukan kai tsaye ga mutane 400 cikin watanni shida masu zuwa.
Babu shakka gwamnatin Masari ta cimma buri uku zuwa hudu a wannan fuska. Da farko ta hana lalacewar jarin da aka fara zubawa a wannan kamfani a shekaru 34 da suka wuce. An samar da kofofin samun aiki ga mutane, musamman matasa da yawa, kuma hakan zai inganta rayuwarsu. Sannan an rage yawan matasan da ke iya fadawa cikin ayyukan ta’addanci da sauran abubuwan da ke barazana ga harkokin tsaro. Sannan burin jawo kamfanoni da ‘yan kasuwa daga cikin gida da kuma kasashen waje domin su zuba jari ya fara cika. A takaice, kuma a jimlace, arzikin jama’ar Jihar Katsina ya ci gaba da bunkasa.

You may also like