Bayanin Gaskiya Ta yadda Faifan Bidiyon Wata Mata Da Wani Mutum Ya Bayyana Suna Sumbatar JunaHIRA TA MUSAMMAN: Yadda Aka Fallasa Bidiyon Wani Sarki Da Matarsa Suna Sumbatar Juna
….mijina na ne na sunnah!
….a Sokoto muke ba Zamfara ba Mijina kuma Basarake ne ba Sanata ba!
….magana na hannun hukuma kuma zasu kamo duk masu hannu wajen yada bidiyon! 
…matakin da zamu dauka akai shine..
…makasudin daukar bidiyon shine….. 
Biyo bayan bullar wani faifan Bidiyo na wata mata da wani dattijo suna sumbatar juna ya jawo cece-kuce da  tofin Allah wadai musamman a shafukan sada zumunta irinsu Facebook, Whatsapp, Instagram da sauransu. 
Shafukan yada labarai da dama sunyi kokarin fadin ainihin abunda ya faru amma ba tare da sunyi nasara ba. 
Majiyarmu ta Hausa Times tayi kokarin bibiyar wannan badakala domin fayyace hakikanin abunda ya faru don fitar da Al’umma daga rudani. Cikin ikon Allah wakilin HAUSA TIMES, Mashkur Ibrahim ya zanta da su wadannan bayin Allah da abun ya faru dasu, kuma ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:-
Tunda farko matar mai suna Hajiya Sa’adatu Muhammad Galadima ta shaidawa HAUSA TIMES cewa “farkon abunda ya faru shine, mijina ne zai yi tafiya to shine sai zamuyi sallama irin na miji da matarsa. To irin kulawa namu na mata sai na karbi wayarshi da nufin in dauki ‘wasan da mukeyi a wayarshi’ don idan ya tafi ya rika kallo yana tunawa dani har Allah yayi dawowarsa.”
Shine fa, Kwatsam bayan tafiyarshi da kwanaki Biyu sai ga kiran waya daga wajenshi yana sanar dani wai abokanansa suna ta kiranshi a waya sun ga bidiyonshi da matarsa ana yadawa a whatsapp. Kan kace kwabo abu kamar da wasa sai gashi ya karade ‘internet’ sai kawai na rika fadin ‘innalillahi Wa’inna ilaihi rajiun”.
Daga bisani kun gano wanda ya fara fitar da bidoyon?
“Gaskiya ba zamu iya cewa ga asalin wanda ya first da bidiyon daga wayar maigidanmu ba har aka fallasa shi. Domin kaga fa akwai ‘password’ a wayar tashi. To kaga abun zai zama kila wani na kusa damu ne. Saboda dama kasan rayuwa baka rasa magauta masu neman ka da sharri”.
Amma ai ance kishiyarki ‘Lubabatu’ ce ta fara fitar da bidiyon, kuma ana zargin tayi haka ne saboda kishi, me zaki ce? 
To, wannan dai zargine kuma ni bani da wata kishiya mai suna ‘Lubabatu’ kuma kaga mu Uku ne a wajen mijin namu,  to wacce ce daga ciki za’a ce ta fitar da bidiyon? Kawai dai bayan barin maigidana yaje sauran gidajen kafin ranar tafiyarshi. Abunda nasani kenan. Kuma ko ma waye mun barshi da Allah. Allah ya isa tsakanimu dashi don wannan tozarci ne. 
Yaya batun zargin da akeyi cewa ke ce kika turawa sauran matan domin su gani. Kuma mecece manufar yin hakan? 
Subahanallhi,  wallahi Allah shine shaida ni ban turawa kowa daga cikinsu bidiyon ba. To me zai sa ma nayi haka bayan dukkanmu muna kokarin yin gasa wajen kyautatawa mai gidanmu domin kowace ta ga itace ta zama zakara a wajen shi.  Kaga idan nayi haka ai na bayyana masu sirrina kenan. 
Amma ke wa kike zargi? Musamman cikin su matan tunda kince ‘kuna gasar zama zakaru a wajen mijin naku? 
Gaskiya ban sani ba.
To a cikin matan wacce ce baku yawan jituwa da ita? 
Ita ta biyun. Domin nice amaryarsu (ta Uku).
Wani faifan murya wato ‘audio’ da kuma wani ‘Chat’ yayi yawo a internet wanda wata Mace ke magana a ciki sannan shima a chat din sun nuna kina zargin mace ta biyun kuma dashi ake ta kafa shaida cewa kina zarginta. Me zaki ce akai? 
Mashkur kenan,  ba zaka gane ba.  Amma ai na fada maka cewa bama jituwa da ita.  Don dai kai ba mace bane shi yasa baka san me naji ba lokacinda abun ya fita…..
Kece kika yi magana a ‘Voice din kenan’ da ‘sceeen shot din chat din’ ? 
Eh to ni dai na yi fada da farko saboda raina ya baci shi yasa mukayi cacar baki da ita.  Abunda nasani kenan. 
An ce mijin naki tsohon Sanata ne daga zamfara yaya gaskiyar abun yake? 
Wallahi haka muma mukaji amma gaskiya ba haka bane,  ni mijina ma Sarki ne, ya karbi sarautan garinsu bayan rasuwar mahaifinsa, sunan garin Bodinga a nan jihar Sokoto. Yanzu haka da muke magana da kai ina nan Sokoto ne. 
Bayan bullan faifan bidiyon me ya biyo baya, musamman jin cewa Mijin naki Basarake ne? 
To,  me zamu yi sai dai add’ua da Allah ya isar mana. Mun barwa Allah komi kuma muna zaman mu lafiya tare da miji na.
 Kenan babu wani mataki da kuke shirin dauka akai?
Eh gaskiya mataki kenan mun sanar da hukuma halin da ake ciki, kuma kamar yadda na shaida maka mijin nawa basarake ne, ita da kanta masarauta da hadin guiwar jam’ian tsaro suna bincike akai. Kuma ko su waye zasu shiga hannu da yardar ubangiji kuma zasu sha hukuncin da ya dace dasu….
To masu yada bidiyon fa? 
Shine nace maka duk zasu hadu da hukuma domin mun kai korafi kuma ana bincike in Allah yaso nan bada jimawa ba masu yadawa da masu sakawa a waya duk zasu shigo hannu.  Kuma zamu neme ku yan jarida ku ga zahiri. Domin jam’ian tsaron suna ta bin shafukan sada zumunta suna tace masu saka bidiyon. Kawai dai a saurari mai zai biyo baya. 
Kafin mu karkare wannan gajeruwar tattaunawa, Bari in dan koma baya kadan. Shin ku nawa ne matan Mai martaba? 
Mu Uku ne. Ai na fada maka a baya. Amma kayi hakuri ba zan baka sunayensu ba. Kamar yadda ban baka sunan na mai martaba ba. Saboda yanayin tsaro. 
Binciken da wannan jarida tayi ta gano cewa aurenki da shi mai martaba bai wani jima ba. Meye gaskiyar batun? 
Eh, to ni amarya ce a wajenshi domin kwata kwata aurenmu bai wuce wata daya da yan kwanaki ba. Munyi aure 17th ga watan Nuwamban shekarar nan. 
A karshe wane sako kike dashi ga daukacin jama’a?
 Ina so in kara tuna masu makasudin daukar bidiyon, a wayar mijina na dauka a matsayin bankwana domin idan ya kalla ya rika tunawa dani. 
Don haka zance don Allah su tayamu hana yada wannan bidiyo. Ko kadan ba’a yishi da wata manufa ta nuna futsara ba. Mu ma’aurata ne kuma a sirrance mukayi. Don Allah a goge a daina yadawa kuma a tayamu da addu’a. Kowa dai yana da Uwa, yana da mata, yana da kanwa, yana da ‘yaya kuma yana da yara,  to don Allah ya zakaji idan akayi masu haka.  To kaga ni da mijina iyayen wasu ne, ni matar wani ce, sannan diyar wani ce kuma kanwar wani ce don Allah ku tayamu hana yada wannan bidiyo domin kare martabarmu da ta diyanmu.  Kowa ya rufawa dan uwanshi asiri shima Allah zai rufa masa. *kuka*
Mun Gode, Hajiya Sa’adatu. 
muma mun gode. 
To jama’a kun dai ji yadda hira ta kasance tsakanin wadannan bayin Allah. Da kuma irin matakin da suke shirin dauka. Don Allah a yada wannan tattaunawa domin fitar dasu daga zargi da kuma hana cigaba da yada bidiyon. In sha Allah RARIYA za ta cigaba da bibiyar wannan badakala. 
Mun yi kokarin jin ta bakin mai martaba sarki amma abun yaci tura. Sai dai yace masarauta na bitar badakalar kuma zata fitar da sanarwa akai.

You may also like