Bayanin Jawabin Buhari Kan shirin Samar da Takin Zamani Da Karancin Abinci


A yau Juma’a ne, Shugaba Buhari ya sadu da kwamitin Shugaban kasa kan shirin raba takin zamani inda ya yabawa kwamitin musamman Gwamnan Jigawa da Shugaban kungiyar masu samar da takin zamani na kasa da shirin da gwamnatinsa ke yi na shawo kan matsalar karancin abinci.

A cikin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya nuna cewa ya gamsu da shirin samar da takin zamani wanda ya kaddamar bayan sun kulla yarjejeniya da Sarkin Moroko a watanni 15 da suka wuce inda ya ce, tun a wancan lokacin yake sa ido sosai kan shirin samar da takin zamanin.

Ya ci gaba da cewa a zamanin gwamnatin da ta wuce, ana samu rahotanni yadda tireloli dauke da takin zamani kan yi layar zana amma a wannan karo babu daya daga cikin tireloli 3,333 da suka yi jigilar takin zamanin da ta bace inda ya ce gwamnati za ta ci gaba da bayar da cikakken tsaro ga wannan shiri.

Ya kara da cewa Babban Bankin Nijeriya ya hada kai da ma’aikatar gona ta tarayya da jihohi wajen bunkasa harkar noma ta yadda Nijeriya ba za ta sake komawa gidan jiya ba na dogaro da kasashen wajen shigowa da abincin da al’ummarta ke bukata.

Buhari ya kuma jaddada gaggauta fara samar da takin zamanin saboda damina ta fara shigowa sannan kuma nan bada jimawa ba, manoman Kudanci za su fara aikin gona inda ya nemi ma’aikatar kudi ta hada kai da gwamnoni don ganin ta samar masu da adadin takin da suka nuna suna bukata.

A karshe Buhari ya nemi Babban Bankin Nijeriya kan ya hada kai da bankuna don ganin an samarwa manoma da kudaden rance sannan ya kalubalanci jami’an tsaro kan su tabbatar takin zamanin ya kai ga wadanda aka tanade shi domin su.

You may also like