
Asalin hoton, Getty Images
FC Bayern Munich ta sanar da daukar Michael Rechner a matsayin mai horar da masu tsare ragarta.
Mai shekara 42 ya koma Bayern daga SG Hoffenheim.
Rechner ya fara aiki da TSG Hoffenheim daga 2008 ya kuma fara horar da masu tsare ragar babbar kungiyar daga 2015, zai yi aiki tare da Julian Nagelsmann.
Rechner ya fara aiki tare da Nagelsmann tsakanin 2013 zuwa 2019, sannan suka koma RB Leipzig.
Bayern tana matakin farko a kan teburin Bundesliga da maki 40 da tazarar maki daya tsakaninta da Union Berling, wadda take ta biyu.
Ranar Asabar Bayern za ta karbi bakuncin VFL Bochum a karawar mako na 20 a Bundesliga.
Wasan farko da suka hadu a bana a babbar gasar tamaula ta Jamus, Bayern ce ta ci 7-0.