Bayyanar Nyass A Wurare Karama Ce Ta Waliyyai – Sheikh Dahiru Bauchi


Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Bauchi, wanda shi ne “Halifan” Shekh Ibrahim Nyass, kuma ya yi ikirarin cewa bayyanar Sheikh Nyass a wurin maulidin da aka kammala a Abuja wata karama ce” wacce Allah ya ke bai wa waliyyansa.

Ya kara da cewa hakan ba wani abin mamaki ba ne domin a nuna wa mutane cewa karamar waliyyai gaskiya ce. Ya ce, “ana iya ganinsa a ko’ina. A daki ma wadansu sun sha ganinsa, ya kan bayyana haka kawai, wannan ba abin mamaki ba ne, karama ce kawai”. Ya kara da cewa su waliyyai suna iya yin abubuwan da sauran mutane ba za su iya yi ba.

You may also like