BAZAMU TABA MANTA ZALUNCIN DA GWAMNATIN BUHARI TAYI MANA BA – INJI MABIYA SHI’ADaruruwan Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky ne suka yi wa babban birnin tarayya Abuja tsinke domin gudanar da muzahrar neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake tsare da shi tun watan disambar 2015. Inda masu mazaharar suka ce har abada ba za su daina bayyana irin zaluncin da gwamnatin Buhari ta yi akan Sheik Zakzaky ba.

An dauko Muzaharar ne tun daga Kasuwar Wuse inda aka tsallake ‘Sky Memorial’ aka kuma naushi Begger.

Masu mazaharar suna tafiya cikin tsari tare da rera wake mai taken a saki jagoran harkar musulunci Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda ake tsare da shi.

You may also like