Tsohon Gwamnan Legas kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinibu ya jaddada cewa babu yadda zai iya maye gurbin Yemi Osibanjo a matsayin Mataimakin Shugaban kasa idan har APC ta sake kafa gwamnati a 2018.
Tinubu ya ce, al’ummar Nijeriya na matukar alfahari da irin kwazo da cikakken hadin kai da Osibanjo ke baiwa Shugaba Buhari a kokarin da suke yi na ceto tattalin arzikin kasar nan ta yadda talaka zai samu walwala.