BBC Hausa: Cin zarafin dan wasa matsala ce ga kwallon Sifaniya – Ancelotti



Vinicius Junior

Asalin hoton, Getty Images

Cin zarafin da ake yi wa dan wasan Real Madrid, Vinicius Junior matsala ce gabaki dayan kwallon Sifaniya in ji Carlo Ancelotti.

Sau uku ana cin zarafin dan wasan Brazil, mai shekara 22 a kakar bana a Sifaniya.

An dauki bidiyon magoya bayan Mallorca a lokacin da suke kalaman cin zarafin dan wasan a karawar da aka ci Real 1-0 ranar Lahadi.

”Ban san dalilin da ake cin zarafin Vinicius ba, ya kamata a magance matsalar, ”in ji Ancelotti.



Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like