BBC Hausa: Mu na neman afuwan ‘yan Najeriya kan karancin man fetur – NNPCMele Kyari

Asalin hoton, MELEKYARI/NNPC

Shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPC ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan matsin da suka sake tsintar kansu sakamakon karancin man fetur.

Shugaban kamfanin man, Mele Kolo Kyari ya tabbatar wa BBC cewa ana sa ran matsalar ta yanke cikin ƴan kwanaki kaɗan masu zuwa.

Kalaman Mele Kyari a tattaunawar sa da BBC, na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma a Najeriya ke ci gaba da fuskantar dogayen layukan mai, musamman a manyan biranen ƙasar.

Matsalar ta man fetur, wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tun a shekarar da ta gabata, na ci gaba da jefa al’ummar Najeriya cikin garari, yayin da babban zaɓen ƙasar ke ƙaratowa.Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like