Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, shugaban ƙasa Janar Muhammadu Buhari da ƴan fadar sa sun sa BBC Hausa a gaba suna masu yi musu magiya kada su ci gaba da sanya ƙarashen hirar d suka yi da mai ɗakinsa Aisha Buhari. Dama gobe ne sashen Hausa na gidan rediyon BBC ya yi alƙawarin sa ƙarashen hirar.