Benzema zai tsawaita zama a Real Madrid, AC Milan na son BalogunBenzema

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon shugaban Leeds Jesse Marsch ya musanta karɓar tayin aiki daga Leicester City, duk da yake, suna gab da kammala tattaunawar ƙarshe kan kwanturagin aiki da shi. (Telegraph – subscription required)

AC Milan ta sanya mai kai hari na Ingila ajin ƙasa da shekaru 21 Folarin Balogun, wanda ke zaman aro a Reims daga Arsenal cikin jerin sunayen ‘yan wasan da take son ɗauka a sabuwar kakar wasanni, duk da yake tana jin Gunners ka iya neman sama da yuro miliyan 30 a kan ɗan wasan. (Calciomercato – in Italian)

Tottenham ta nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan Moroko, Hakim Ziyech, mai shekara 30, daga Chelsea wadda yake takawa leda. (Football Insider)

Manchester United na bibiyar ɗan wasan Celta Vigo, kuma na tsakiyar Sifaniya Gabri Veiga, mai shekara 20, kafin buɗe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a kaka mai zuwa. (Football Insider)Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like