Bernard Arnault: Abu biyar da suka kamata ku sani game da sabon mutumin da ya fi kuɗi a duniya



Bernard Arnault

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bernard Arnault ya tara dukiyarsa daga kamfanin LVMH da ya mallaka

A makon da ya gabata ne Elon Musk ya sauka daga matsayi na ɗaya a jerin masu arziki na duniya baki ɗaya bayan raguwar darajar hannun jari a kamfaninsa na Tesla.

A cewar mujallun Forbes da Bloomberg, Bernard Arnault ne ya sauke Mista Musk daga matsayin, wanda shi ne shugaban kamfanin ƙera kayan ƙasaita na LVMH.

Mista Musk ne ke da mafi girman hannun jari a kamfanin ƙera motoci masu aiki da lantarki na Tesla, inda yake da kashi 14 cikin 100.

A cewar Forbes, dukiyar Mista Musk yanzu tana wajen dala biliyan 178. Shi kuwa Bernard Arnault na da biliyan 188.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like