
Wata mace yar kunar bakin wake da ake zaton yar kungiyar Boko Haram ce ta tarwatsa kanta a bakin wani masallaci dake yankin Fulatari a Buni Yadi dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe a ranar Juma’a inda suka kashe mutane 7.
Harin na Yobe na zuwa ne Kasa da mako biyu bayan da aka sace wasu yan mata 110 a makarantar sakandaren Yan Mata Ta Kimiyya Da Fasaha dake Dapchi.
Wata majiya a rundunar soji ta shedawa jaridar The Cable cewa harin ya faru ne da misalin karfe 5:30 lokacin da aka taru domin yin sallar asuba.
A cewar majiyar an dauke wadanda suka jikkata ya zuwa asibiti.
“Fashewar bom din gaskiya ne, sun rasa mutane 7 a harin, 28 kuma suka jikkata.ya faru da safiyar nan lokacin sallar asuba da misalin Æ™arfe 5:30. Akwai wadanda suka jikkata da dama har yanzu suna daukar su zuwa asibiti. Iya kacin abinda zan iya cewa kenan a yanzu,” a cewar majiyar.