Akwai wagegen giɓi tsakanin ɗalibai maza da mata a dukkan fannoni na kimiyya da fasaha har ma da lisafi a dukkan sassan duniya.
Amma duk da cewa mata sun sami gagarumin ci-gaba a fagen shiga cikin masu ilimin gaba da na sakandare, har zuwa yau akwai bukatar shigar da karin mata masu yawa a wadannan fannonin.
A ranar 20 ga watan Disambar 2013, babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri na ba mata damar samun daidaito da maza a dukkan fannoni na kimiyya da fasaha, inda ya ce wannan matakin zai taimaka wajen ‘yantar da mata da ‘yan mata.