Bikin Ranar Yara Ta Duniya
Ranar ta yau an yi mata lakabin kowanne yaro yana da ƴanci daidai sauran yara ƴan uwansa. A Najeriya, yara sama da miliyan 10 ne ba sa zuwa makaranta kuma wannan naƙaso ne ga kasar.

Kowane yaro yana da yanci kamar kowa” itace taken ranar ya yara ta bana, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware wanda hakan yana nuni da cewa hakkin kowane yaro ne ya samu kulawa da kuma ba shi ilimi daidai gwargwado.

Ƙididdigar Hukumar Asusun Yara ta Duniya wato UNICEF ya nuna cewa yara sama da miliyan 10.5 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya, akasarinsu daga Arewacin ƙasar, kuma Najeriya na daga cikin ƙasashe na gaba-gaba dake da wannan rinjaye a duniya.

Shin ko yaya masana ke ganin illar rashin sanin makomar irin waɗannan yara? Dakta Abdullahi Kashere, manazarci ne kuma Malami a Jami’ar Tarayya dake Kashere Jihar Gombe ya shaida cewa “wannan babbar barazana ce ga ƙasar kanta, saboda ɗorewar ƙasa ya dogara ne da yadda yara ke sanin makomarsu, kuma idan ba’a basu ilimi me nagarta ba, makomarsu barazana ce ga ƙasa.”

A hirarsa da Muryar Amurka, Abubakar Usman, wani mai sharhi ne a kan abubuwan yau da kullum ya ce “barin irin waɗannan yara suna barace-barace ko kuma tallace-tallace ba tare da kaisu makaranta ba, illa ce ba ƙarama ba, domin a ƙarshe za su kasance masu ta’ammali da muggan ƙwayoyi ko kuma su faɗa hannun muggan mutane.”

Abubakar ya ƙara da cewa “kamata yayi dukkanin sassan gwamnatin su ɗauki alhakin baiwa irin waɗannan yara kulawa, domin ta haka ne za’a iya kaiwa gacci cikin nasara.”

Yanzu dai hankula sun koma ga mahukunta domin ganin irin matakai da zasu ɗauka domin kaucewa irin waɗannan ƙalubalai da ake ganin ka iya kassara mafarkin ƙasar.

Saurari rahoton Ruƙaiya Basha:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like