Bikin Sallah :Gwamnatin jihar Lagos Zata Cika Kasuwannin Jihar Da Shinkafa Mai Saukin Kudi


Hoto: Daily Trust

Gwamnatin jihar Lagos ta sanar da kawo tirelar 70 ta shinkafar da ake kira LAKE RICE domin amfanin mutanen jihar a  bikin babbar Sallah,gwamnatin jihar ce ke samar shinkafar  da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kebbi.

 A wata sanarwa da wani babban jami’i a ma’aikatar aiyukan gona ta jihar,Tunbosun Ogunbawo, ya fitar yace za  a fara sayarwa da jama’a shinkafar daga yau ranar Alhamis.

  Sanarwar ta rawaito kwamishinan aikin gonar jihar Toyin Suarau na cewa gwamnatin jihar tayi cikakken tanadi don ganin cewa mutanen jihar dake son siyan shinkafar sun siya ba tare da wahala ba.

” Wannan gwamnatin ta tanadi duk abinda ake bukata,tireloli suna shigowa da shinkafar. A yanzu da muke magana  akwai sama da motoci 30 dauke da shinkafar dake cikin Lagos, nan da ranar Juma’a za su zama 40, nan da sati mai zuwa zasu zama 70 ko bayan bukukuwan sallah akwai shinkafar  da yawa da za a kawo cikin Lagos, ” Kwamishinan yace.

Sanarwar ta kara da cewa za a siyar da shinkafar a dukkanin kananan hukumomi 20 dake jihar da kuma  yankunan cigaba 37 dake jihar. 

Za dai a siyar da kowanne babban buhu mai  nauyin kilogiram 50 na shinkafar kan kudi naira 12000 yayin da karamin buhu mai nauyin kilogiram 25 za a siyar dashi naira 6000.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like