Kungiyar Kiristoci Ta Najeriya CAN, ta shawarci musulmin kasarnan da su rungumi tsarin rayuwa irin ta annabi Ibrahim.
Tunde Akinsanya shugaban kungiyar a jihar Ogun yayi wannan kiran a wata sanarwa da sakataren yada labaransa,Tolulope Taiwo yafitar jiya Alhamis a birnin Abeokuta domin taya yan alummar musulmi barka da Sallah.
Akinsanya ya taya musulmin kasarnan baki daya murna musamman ma na jihar Ogun.
Ya Godewa Allah da yasa Najeriya ta cigaba da zama kasa daya duk da kalubalen da take fuskanta.
Ya kuma godewa Allah da yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari cikakkiyar lafiya da kuma damar yin bikin Sallah tare da mutanensa.
” Ina so musamman na taya jagoran musulmin Najeriya, mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Saad Abubakar, da kuma gwamnan jihar Ogun Ibikunle kan yadda Allah yasake nuna mana wannan lokaci na farin ciki da kyauta.
” Kiristoci na kira ga dukkanin Musulmi da su rungumi rayuwa irin ta annabi Ibrahim wanda ya zabi ya sadaukar da dansa ga Allah.”
Yayi kira ga yan Najeriya kan su hada hannu da gwamnati a dukkanin matakai domin samar da shugabanci nagari.