Bikin Yaye Dalibai A Kwalejin Sa’adatu Rimi


saa

 

  • Baje Kolin Tarbiyya Ko Rashin Tarbiyya?

A makon da ya gabata ne daliban kwalejin Ilmi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, sashen Taba Kida Taba Karatu (Part Time), suka yi bikin bankwana da

makarantar. Babu shakka bikin ya zo da tsarabobi kala daban-dabaan, inda kida ya rika tashi ta ko’ina babu ji ba gani, inda a hannu guda kuma daliban suka gwamutsa mazansu da manta suka rika rawa suna cashewa, abin dai kawai sai wanda ya gani.

Babban abin takaicin shi ne, kafatnin daliban nan aka rasa wanda iya yin tunanin tsawatarwa ko tunawa da al’ada ko addini, musamman daliban da suka fito daga sashen harshen Hausa da turanci, su ma bin Yarima suka yi suka sha kida mazansu da matansu.

Duk da cewa irin wannan biki an saba gabatar da shi a duk karshen shekara, daidai lokacin da dalibai za su fita ko kammala karatunsu, amma fa a wannan karo bikin ya sha bamban da mafi yawa daga cikin bukukuwan da daliban suka aiwatar.

 

Kamar yadda muka samu tattaunawa da wasu tsoffin dalibai da kuma sabbin daliban makarantar wadanda suka nemi a sakaya sunansu, sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:

“A tunanina idan har aka ce daliban makarantar ilmi za su fita, to kamata ya yi a ce abin ya zama na musamman tunda dai ana kyautata zaton

malamai ne wadanda za su jagoranci al’umma da kuma wani sashi na makarantu don bayar da tarbiyya da kuma ingantaccen ilmi kamar dai yadda ake sa ran sun samu kyakkyawar tarbiyya daga wannan makaranta wadda ake kira Kwalejin ilmi, sai kuma gashi abin ya sha bamban daga abin da suke aikatawa a zahirance, bikin da ko a kasar Italiya aka yi shi an san cewa babu shakka watsewar ta kai watsewa.

Wani abin mamaki da idanunawana suka nuna min shi ne, yadda malaman makarantar suka zama ‘yan kallo da kuma nishadantuwa da al’amarin ta hanyar daukar hotuna da sauran daliban maimaikon a ce sun tsawatar daga halin rashin da’ar da daliban ke aikatawa, tambaya a nan ita ce anya kuwa wannan makarantar ta kwalejin ilmi ce? Amma dai da dukkanin alamu jagoran wannan makaranta bai san cewa wadannan dalibai sun aikata wannan aikin masha’ar ba, duba da yadda yake kula da sha’anin tarbiya da addini a wannan makaranta.

Duk da cewa akwai malaman makarantar a wurin, ba su kuma tsawatar ba.

Wasu daga cikin daliban makarantar ‘yan kungiyar addinin Musulunci sun bayyana min cewa shugaban makarantar na da akidar kin ganin cakuduwa tsakanin maza da mata guri guda, to kenan a nan sai a ce, “albasa ba ta yi halin ruwa ba”.

Jihar Kano ta samu kyakkyawan yabo daga tsabtar tarbiyya da kuma kyakkyawar shiga, sannan wannan kwaleji ta Sa’adatu Rimi tana daya daga cikin manyan makarantu da gwamnati ke ji da ita, za a fahimci haka daga yadda ake inganta makarantar ta hanyar zamanantar da ita da sabbin gine-ginen zamani. Haka kuma babban abin da idanunka za su fara tozali da shi yayin da ka shiga makarantar shi ne allon sanarwar kiyaye shiga ta tufafi da kuma da’a.

Shin hakan dama”Bigi ba giro ne? duba allon duba rudu” Ko kuma akasi aka samu?

Gaskiyar magana ya kamata a ce hukumar wannan makaranta ta kafa wani kwamiti  wanda zai rika lura da irin wadannan bukukuwa da ake gabatarwa a duk karshen shekara musamman, don kare martabar ilmi da kuma mutuncin jihar Kano kasancewar bikin yana samun halartar dangi da iyayen daliban. Don kuwa matukar aka bari hakan ya ci gaba da faruwa, al’amarin ba zai haifar da da mai ido ba, musamman yadda wasu ke fadin bikin wannan shekarar ya fi na sauran shekarun baya yanayin sheke aya da kuma aikata masha’a karara.

You may also like