Bincike: Akwai yiwuwar halittun sama su fara neman kalaci a duniyarmu


 

Malaman kimiyya da suka yi nazari kan taurari miliyan 2.5 sun fitar da sakamakon farko wanda ya janyo tattauna batun a duniya.

Hamshakin maikudinkasar Rasha Yuri Milner da mai kamfanin Facebook Mark Zuckerberg ne suka dauki nauyin gudanar da binciken wanda farfesan Birtaniyakan fannin Kimiyya da Fasaha Stephen Hawking ya jagoranta.

Sanarwar da aka fitar na cewa, daga cikin taurarin miliyan 2.5 an gano wasu 234 da ba daidai suke ba.

Sanarwar ta kuma ce, akwai yiwuwar samun sakafa daga duniyoyin sararin samaniya.

Hawking ya samar da wani ilimi wanda ba na lissafi ba da ya ke nuna yiwuwar akwai rayuwa a wata duniyar da ba tamu ba.

Malamin Kimiyyar ya taba yin gargadi a baya cewa, halittun da suke saa na iya zama karshen rayuwar bil’adama dake duniyarmu.

Ya ce, halittun da ke cikin wadannan duniyoyi na sama za su kammala cinye komai na duniyoyin nasu wanda hakan zai sa su nemi abinci daga tau duniyar.

You may also like