Bincike Da Tuhumar Masu Kisan Gilla Zai Kawo Hadin Kan Kasa-Sarkin MusulmiWannan na zuwa ne lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin kisan gilla ga jama’a a yankunan da ba nasu na asali ba, abinda mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci jama’a da su kai zukata nesa.

Shugaban Majalisar koli akan lamurran addinin musulunci a Najeriya mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa akan yadda kafafen sada zumunta na yanar gizo ke ruruta irin wadannan matsalolin.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. Bisa ga cewarsa,

“abinda ya faru a jihar Anambara, abu ne na dabbanci kuma mummuna a yanke macce da ‘ya’yanta wadanda basu ji ba basu gani ba, wai saboda bambancin kabila ko addini, wannan abin yana nuna kamar muna yaki da juna ba a fagen daga ba a kafafen sada zumunta na yanar gizo, ina son ince idan har wannan abin haka yake, na yi magana da gwamnan jihar Anambara Charles Soludu da wasu jagororin yankin akan wannan batun kuma na gamsu da matakan da suke dauka na shawo kan tashe tashen hankulan jama’a a yankin na gabacin Najeriya don mu zauna lafiya da juna, mu muna kula da duk wanda ya zo ya zauna cikin mu don haka muna son muma a kula da namu mutane dake zaune a wasu wurare”.

Ziyarar Mataimakin Shugaban NajeriyaYemi Osinbajo fadar Sarkin Musulmi

Ziyarar Mataimakin Shugaban NajeriyaYemi Osinbajo fadar Sarkin Musulmi

Mataimakin Shugaban Najeriya farfesa Yemi Osinbajo wanda ya ziyarci fadar ta mai alfarma sarkin musulmi a wata ziyarar da ya kai Sakkwato cikin daren jiya Talata, ya aminta da cewa lallai hadin kan kasar ne kawai zai iya tsirar da ita da kuma ci gaba da rike martabar ta a idanun kasashen duniya.

Ya ce, “Hadin kasar nan ne yasa take da kima a idanun duniya kuma dole ne mu rike wannan martabar, kar mu yarda da duk abinda kan kawo illa ga hadin kan mu, wannan ce hanyar da ya kamata mu zauna kasar nan, kasa wadda ke da mabambantan addinai da kabilu, kai ko wadanda basu yi imani da ko wane abin bauta ba in ‘yan Najeriya ne dole mu zauna tare”

Mataimakin shugaban Najeriyar ya je Sakkwato ne domin ganawa da wakilan da zasu yi zaben fitar da ‘yan takara na jam’iyar APC kasancewar sa daya daga cikin masu neman tsayawa takarar shugabancin kasar.

Najeriya ta kasance kasa wadda ke da al’ummomi masu mabambantan addinai da kabila wadanda ke zaune a wuri daya shekaru da dama.

Wani abu da kan daure kan ‘yan Najeriya shine jagororin al’umma sun jima suna da’awar zaman lafiya tsakanin jama’a amma kuma hakan bai hana samun tashin hankali idan wani abu ya faru.

Duk da da’awar zaman lafiya da juna da manyan addinan kasar ke koyarwa ga mabiyan su wasu lokuta akan samu tashe tashen hankula sanadiyar addini ko kabila.

Saurari cikakken rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti:

You may also like