A ‘yan shekarun da suka gabata,a wata makala mai taken “Polio ce tushen kanjamau” wadda aka wallafa a Jaridar Reuters,wasu masu bincike na yammacin duniya sun fitar da bayanai game da asalin cutar nan da ke karya garkuwar jikin bil adama wato Aids..
Mutanen sun bayyana cewa,cutar kabari salamu alaikum ta samo asali ne daga allurar polio wadda aka sarrafa ta hanyar amfani da tsokar jikin goggon birin kasar Kongo mai kunshe da kwayoyin halittar SIV.
Wadannan kwayoyin halittun ne suka rikida domin komawa HIV a lokacin da aka yi amfani da allurar kan al’umar Kongo.
Tun a wannan zamanin ne allurar cutar sha’inna ta fara zama abin kyama a wasu kusurwowin duniya musamman ma a kasashen Musulmai kamar su Afganistan,Pakistan,arewacin Najeriya da dai sauran su.
A wadannan kasashen masu allurar Polio da dama sun rasa rayukansu,sakamakon irin kwallon aka dinga yi musu na masu leken asiri ko kuma wadanda suka yi shigar burtu domin taimaka wa Turawa a wajen hana yara haifuwa a nan gaba.Abinda yasa aka ci gaba da samun koma baya a rigakafin wannan annobar da ta adabbi yara kanana.
A wasu kasashen ma,shugabanni na yin amfani da karfin iko domin tirsasa uwayen yara a wajen yi wa ‘ya ‘yansu allurar Polio.
Masana daga sassa daban-daban na duniya na ci gaba yin aiki tukuru, domin ganin sun kawar da wannan bakar fahimtar da duniya ta yi wa Polio da kuma jita-jitan da ke ci gaba da yaduwa dangane da cutar.
A ranar 13 ga watan Mayun shekarar 2002,wasu masana a fannin ilimin kananan halittu wato ”Microbiology” a Turance na kasar Faransa,sun karyata wannan batun tare da kawo cikakkun bayanai,inda suka tabbatar da cewa maimakon namar goggon biri da aka bayyana a baya, tsokar karamin biri ne aka yi amfani da ita a wajen hada allurar Polio. A jikin wannan dabbar kuma babu kwayar cutar SIV.
Wasu sabbin Hujjojin da malamin jami’ar Arizona Dr. Michael Worobey ya wallafa a baya baya nan sun jaddada cewa kwayar cutar da ke jikin goggon birin Kongo bata da wata alaka da wadda a yanzu haka ta yadu a tsakiyar al’umar kasar.Kuma an fara gwaje-gwajen farko na allurar Polio a kasar ta Kongo shekaru 30 bayan bullowar cutar kanjamau.
Abinda ke nuna cewa babu wata alakar da ke tsakanin cutar Shan inna da kanjamau.Haka zalika,allurar Polio bata hana haifuwa ko kuma haddasa wata illa makamanciyar haka.