Kimanin Mata masu juna 94,141 suke dauke da cutar kanjamau a jihar Zamfara. Kamar yadda Hukumar tallafawa masu cutar ta majalisar dinkin duniya (PRO-ACT) ta tabbatar. Jagoran shirin Aminu Sarki, ya bayyana haka ne a yayin taron shekara bakwai na tallafawa masu cutar a garin Gusau.