Bincike: ‘Ya ‘yan mazan da ke auren mace fiye da daya sun fi hazaka


 

 

Binciken da wasu masanan kasar Ingila suka yi ya nuna cewa yaran da gyatuminsu ke auren mace fiye da daya sun fi hazaka da walwala.

Masanan sun gudanar da bincikensu a akalla muhallai 350 na kashen Kenya da Tanzania,inda suka gano cewa mazan da ke da mata sama da daya sun fi arziki, haka zalika zuri’arsu ta fi ta wadanda ke da mace daya tilo kwanciyar hankali da koshi.

Abinda yasa suka gargadi kungiyoyin da ke fafutukar yaki da auren fiye da mace daya da su sake yin tunani.

A yayin da yake magana a gaban manema labaran kafar yada labarai ta Reuters,masani David Lawson na cibiyar tsaftace muhalli da yaki da cututtukan da ke da alaka da yankuna masu zafi da ke a London, ya kara da tabbatar gaskiyar wannan binciken.

You may also like