Binciken gwamnatin Kano ya wanke Ado Doguwa daga zargin kisan kaiAlhassan Ado Doguwa

Asalin hoton, TWITTER/ADO DOGUWA

Bayanan hoto,

Alhassan Ado Doguwa

Ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta bayyana cewa binciken da ta gudanar kan tuhumar da ake yi wa ɗan majalisar wakilan Tarayya, Alhassan Ado Doguwa kan laifn kisan, ya nuna cewa ba a same shi da laifin da ake zargi ba.

Lokacin da ya yi wa manema labarai bayani, kwamishinan shari’a na jihar Kano, Lawan Musa Abdullahi ya ce an samu saɓani da dama cikin bayanan da aka samu daga wurin shaidu.

Ya ƙara da cewa a yayin da suke gudanar da bincike sun gano cewa ma’aikatan asibiti ba su yi cikakken bincike kan mutanen da ake zargin an harba da bindiga ba, soboda haka ba a iya tabbatar da cewa an harbe su ba.

Kwamishinan ya bayyana cewa an gudanar da bincike kan bindigogi da harsashai da ke hannun ‘yan sandan da ke tare da ɗan majalisar a lokacin da rikicin ya faru kuma babu wata shaida da ta nuna cewa an yi amfani da bindigogin, kasancewar jami’an ƴan sandan sun mayar da daidai adadin harsasan da ke a hannunsu.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like