Binciken Masana Ya Tabbatar Da Cewa Tsawaita Zama Kan Kujera Na Dakushe Kwakwalwa


Sakamakon wani sabon bincike na kwararru ya nuna cewa zama kan Kujera na tsawon lokaci don kallon talbijin na dakushe kwakwalwa ta yadda mutum zai rika saurin yin mantuwa da tunani mara tasiri.

Binciken ya nuna cewa mutanen da ke da irin wannan dabi’a na jimawa kan Kujera don kallon talbijin za su iya fuskantar yanayin damuwa a rayuwa ba ya ga matsala a harshe ko da kuwa suna motsa jiki.

You may also like