Bindigar Wani Jami’in DSS Tayi Harbi Bisa Tsautsayi A Fadar Shugaban Kasa


SHUGABA Muhammadu Buhari

Rahotanni daga fadar shugaban kasa Aso Rock Villa na nuna cewa bindigar wani jami’in DSS ta yi harbi bisa kuskure inda tajiwa wata mata ciwo a cikinta da cinyarta. 

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne a jiya Laraba a dakin tarbar baki na Aso Rock Villa fannin offishin gudanarwa. 
Majiyarmu ta rawaito cewa jami’an tsaron dake kula da harabar ne suka bukaci wani jami’in DSS ya ajiye makaminsa kafin shiga cikin harabar ofishin tarbar bakin a inda yaje ajiya bindigar tasa sai kawai harsashi ya fita inda nan take ya raunata wata mata daya. 
Tuni dai aka garzaya da matar zuwa asibitin dake fadar shugaban kasa domin duba lafiyarta.

You may also like