Birtaniya za ta daina ɗaukan likitoci daga Najeriya...

Asalin hoton, Science Photo Library

Birtaniya ta sanya sunan Najeriya a cikin jerin ƙasashen da ba za ta rinƙa ɗaukan likitoci da masu kula da masu rauni daga ƙasar ba.

Birtaniyar ta ɗauki matakin ne bayan sabunta ƙa’idojinta na ɗaukan ma’aikata daga ƙasashen ƙetare.

A yanzu sunan Najeriya ya faɗa cikin waɗanda aka sanya wa launin ja ko ɗorawa, wanda yake fitowa daga Hukumar Lafiya ta Duniya.

Jerin ƙasashen wanda WHO ke sabuntawa bayan shekaru uku na nufin cewa ba za a ɗauki jami’an lafiya daga irin waɗannan ƙasashe ba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like