Birtaniya Zata dawowa da Nigeria kudin da Aka sata. 


Gwamnatin Birtaniya ta amince za ta mayar wa Najeriya kudi kimanin Fam miliyan 700 daga cikin kudaden da aka sace aka boye a kasar.
A makon nan ne dai kasashen biyu suka rattaba hannu akan wata yarjeniyar tsare-tsaren yadda za a maida kudina Abuja, babban birnin Najeriya.

Ministan shari’a Abubakar Malami ne ya wakilci gwamnatin Najeriya, yayin da Ministan kula da shige-da-ficen Burtaniya, kuma dan majalisar dokoki, Robert Goodwill ya saka hannun a madadin Kasarsa.Ministan shari’ar na Najeriya Abubakar Malami ya shaida wa ‘yan Jaridu cewa wannan adadin kudin shi ne kashi na farko da Birtaniya ta amince za ta mayar wa Najeriya.

Ya ce ana ci gaba da bincike kan gidaje da kadarori da wasu kudaden da ake zargin an karkatar da su zuwa Birtaniya daga Nijeriya ba bisa ka’ida ba.

Abubakar Malami ya ce a makon gobe ne za a mika wa Birtaniya bayanai kan asusun da ake zargi an ajiye kudaden, inda daga nan kuma za a fara shirye-shiryen mayar wa Najeriyar kudaden.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like