Blinken: Rasha na wargaza tsarin duniya | Labarai | DW Blinken yace mutum guda ya haddasa wannan yaki kuma mutum guda zai iya kawo karshensa saboda idan Rasha ta dakatar da fada yakin zai kare. Idan Ukraine ta dakatar da fada, karshen Ukraine kenan. A saboda haka za mu ci gaba da taimaka wa Ukraine a yayin da ta ke kokarin kare kanta da kuma karfafa mata samun masalaha ta diflomasiyya bisa adalci.

Blinken ya kuma baiyana halin da wani da sojojin Rasha suka ci zarafinsa ya sami kansa a ciki yana mai cewa mutumin yace sojojin sun yi masa duka inda har ya kai baya jin komai.

Sakataren harkokin wajen na Amirka ya kuma zayyana abin da gwamnatin Biden ta yi imani da cewa yakin ba kawai ya haddasa mummunan barna da lalata kasar Ukraine da al’umarta  bane kadai har ma ya haddasa babbar matsala a duniya baki daya da suka hada da yunwa da karancin makamashi.
 You may also like