Bode George ya janye daga takarar zama shugaban jam’iyyar PDP


Olabode George daya daga cikin yan takara 8 dake nema zama shugaban jam’iyyar PDP ya janye aniyarsa ta shiga zaɓen.

George ya bayyana matakinsa na janyewa daga takarar jim kaɗan bayan da kwamitin tantance yan takara ya amince masa ya tsaya takara a zaɓen.

Ya ɗorawa jam’iyar laifin kin ware wani yanki guda da shugaban jam’iyyar zai fito daga ciki inda yace ba ayi wa Yarabawa dake takara a zaɓen ba adalci.

George ya bukaci gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya bashi kan wasu kalamai marasa da daɗi da yayi akan yankin kudu maso yamma.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like