Hukumar ‘yan sandan ciki ta Najeriya ta ce ta kama wani kwararren mai hada wa kungiyar Boko Haram bama-bamai .
An kama shi a lokacin da yake shirya yadda za a dauke shi aiki a rundunar sojin kasa ta Najeriya.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta DSS ta ce an kama mutumin ne sakamakon wani aikin hadin gwiwa tsakanin jami’anta da na rundunar sojin.
Aikin dai ya zo ne bayan samun bayanan sirri da ke cewa mayakan kungiyar na sake tattaruwa a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.
Sai dai Kakakin rundunar sojin Kanal Sani Usman Kukashen ya shaida wa ‘yan jaridu cewa ko ba a irin wannan aikin na hadin gwiwa ba, rundunar na da matakan rigakafin kutsen irin wadannan mutanen zuwa cikinta.