Boko Haram: An Kama Wanda Ya Shirya Kai Hari Babban Masallacin Gidan Sarki Na Jihar KanoHukumar ‘yan sandan farin kaya ta DSS ta kama wani babban kwamandan kungiyar IS dake yammacin Afrika a ranar Asabar, mai suna Husseini Maitangaran wanda ya shahara wajen hada Bama-Bamai da kai manyan hare-hare.

Hukumar ta ce Maitangaran shi ya jagoranci kai hari a ofishin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda (AIG zone 1) dake Kano a ranar 20 ga watan Janairu 2012, tare da harin babban masallacin Jumma’a na gidan sarki a jihar Kano da wata cibiyar bayanai ta sojoji dake Yobe, inda mutane sama da 100 suka mutu a 2015.

Kuma bayanai sun tabbatar da cewar ya taimakawa DSS da bayanai suka kama wasu kwamandojin biyu, Abdulkadir Umar Muhammad da Muhammad Ali duk a jihar Kano, wanda a lokacin suna shirin kai hare-hare a Jihohin Kano, Yobe, Naija, Abuja, da Borno tare da Kanada, a lokutan bukukuwan babbar sallar layya wadda akayi a 1 ga watan satumbar nan wanda basu samu nasarar kaiwa ba har aka samu nasarar cafke su.

You may also like