Abu Musad Al-Barnawi shugaban wani bangare na kungiyar Boko Haram,yace sojojin Najeriya za su samu nasara akan kungiyar dake karkashin jagorancin Abubakar Shekau.
Al-Barnawi yayi wannan hasashe ne a wani fefan bidiyo da aka saka a shafin YouTube.
Yace Shekau ya kauce daga kan ainihin dalilin da yasa aka kafa kungiyar.
Ya ci gaba da cewa Muhammad Yusif, ya kafa kungiyar ne domin yada kyawawan koyarwar addinin musulunci amma yanzu kungiyar ta zama wata hanya ta aikata duk wasu miyagun laifuka.