Boko Haram: Har yanzu yara ba sa zuwa makaranta


 

Fiye da shekaru biyu kenan da aka rufe makarantun gaba da Firamare sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram a wasu yankunan da ke jihar Borno na Najeriya, lamarin da ya sanya duban mutane tsere wa muhallinsu.

Jama’a da dama ne ke samun mafaka a yanzu a sansanin ‘yan gudun hijirah a cikin garin Maiduguri, inda suka mayar da makarantu sansanoninsu

Wannan batu dai ya jawo tabarbarewar ilimin a jihar Borno tare da kuma sanya yara gararamba da tallace-tallace da yawon banza a birnin na Maiduguri.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like