Babban Kwamandan askarawan Nijeriya, Laftar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa zuwa yanzu sun samu nasarar ceto mutane sama da 20,000 da ‘yan Boko Haram ke rike da su daga wurare daban-daban a kasar nan.
Buratai ya bayyana haka ne lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai wajen kaddamar da makarantar da kungiyar matan manyan soji Nijeriya, reshen 1 Dib, (NAOWA) Kaduna suka gina a Barikin sojoji na Ribado da ke Kaduna a ranar Asabar da ta gabata.
Ya ci gaba da bayyana cewa, ba gudu ba ja da baya wajen ci gaba da karbo wadanda ko dai Boko Haram suka sace ko kuma suke tsare da su. Ya ce, duk da kiran da ake yi na sasantawa da ‘yan Boko Haram da ke aikata ta’addanci a area maso gabashin kasar nan, ba zai sa sojojin sanya ba.
Ya ce, kokarin sasantawar da ake yi ba zai dakatar da soji daga yin aikinsu ba, musamman na ceto wadanda Boko Haram ke sacewa ba. Inda ya yi kira ga duk wanda ke da wani bayani da zai taimaka wajen gano wadanda kungiyar ke tsare da su, ya taimaka ya sanar da su.
Daga nan ya yaba wa uwargidan Kwamandan 1 Dibision, Misis Florence Adeniyi Oyebade bisa gina wannan makaranta da ta yi. Inda ya nemi sauran matan manyan jami’an sojojin da su yi koyi da wannan aiki.
A nata jawabin, uwargidan Janar Buratai, Hajiya Ummu Kulsum Buratai, kuma Shugaban kungiyar matar manyan sojojin ta kasa, ta bayyana cewa kungiyarsu za ta ci gaba da yin ayyukan taimako a barikokin sojojin kasar nan, don inganta rayuwar su.
Ita kuwa Uwargidan Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Nasiru El-rufa’i ta bayyana jin dadinta ne, da kuma gamsuwa da ingàncin aiki ganin makarantar. Sannan ta gode wa Uwargida Florence bisa wannan namijin kokari da ta yi cikin shekara guda da zuwansu Kaduna.
Tun da farko sai da Janar Buratai ya ziyarci hedikwatar 1 Dib. da ke Kawo Kaduna. Inda ya gana da manyan jami’an rundunar cikin sirri. Ganawar dai an yi ta ne don bayyana wa Buratai nasarar da rundunar ta samu a cikin shekara guda da Kwamandan rundunar, Manjo Janar Adeniyi Oyebade ya yi yana Shugabantar rundunar.