Boko Haram Na Amfani Da Jarirai Wajen Kai Harin Ta’addanci


wp-1485269929387.jpg

 

 

Mahukutan a Nijeriya sun bayyana cewar mata ‘yan kungiyar Boko haram sun shigo da wata sabuwar dabara ta kai harin kunar bakin wake ta hanyar amfani da jarirai don kar a gano su.

A cikin wani rahoto da gwamnatin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriyan ta fitar ta bayyana cewar mata ‘yan kunar-bakin-waken a halin yanzu  sun fito da wata dabarar tafiya da jarirai wajen wajen kai hare-haren kunar bakin waken don kar a gano su; lamarin da gwamnatin ta ce wani salo ne mai matukar hadarin gaske.

Wannan jan kunnen dai ya biyo bayan wani hari ne da da wasu mata biyu goye da jarirai suka kai garin Madagali na jihar ta Adamawa a ranar 13 ga watan Janairun nan inda suka kashe kansu da kuma wasu mutane hudu.

Su dai wadannan matan sun sami nasarar ketare shingen jami’an tsaro ne saboda suna dauke da jarirai bayan da jami’an tsaron suka zaci su ‘yan gudun hijira ne.

You may also like