Boko Haram Na Shirye Ta Tattauna Da Gwamnati Kan Sake Karin ‘Yan Matan Chibok


4bka51816d2e04fu0p_800c450

 

‘Yan kwanaki bayan sako ‘yan matan makarantar Chibok su 21 da kungiyar Boko Haram ta yi, gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa wani bangare na kungiyar sun sanar da aniyarsu ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin don sako karin wasu ‘yan matan su 83 daga cikin sama da 200 da suka sace sama da shekaru biyu da suka gabata.

 

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce kakakin shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari, wato Malam Garba Shehu ne ya shaida masa hakan a wata tattaunawa da wayar tarho da suka yi inda ya ce ‘yan mata 21 da kungiyar  ta sako kwanakin baya wani kokari ne na wannan bangare na Boko Haram din na nuna wa gwamnatin Nijeriyan cewa suna rike da wasu karin ‘yan matan Chibok din su 83 a hannunsu.

Malam Garba Shehu ya kara da cewa ‘yan wannan bangaren sun sanar da cewa a shirye suke su tattauna da gwamnatin in tana so don sako wadannan ‘yan mata su 83, don haka sai kakakin shugaban ya ce gwamnatin ta su ita  ma a shirye take ta tatttauna da wannan bangaren na Boko Haram din.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce wannan bangare na kungiyar ta Boko Haram ya sako wasu daga cikin ‘yan matan Chibok din su 21 bayan wata yarjejeniya da aka cimma tsakaninsu da kungiyar Red Cross ta  kasa da kasa da kuma gwamnatin kasar Swiss.

Wasu kafafen watsa labarai dai sun ce musayen fursunoni ne aka yi tsakanin gwamnatin Nijeriyan da ‘yan Boko Haram din sai dai gwamnatin Nijeriya n ta bakin ministan yada labaranta Lai Muhammad ta musanta wannan labarin inda ta ce ba musayar fursunonin ta yi da kungiyar Boko Haram ba. Lai Muhammad ya ce ‘yan Boko Haram din sun sako ‘yan matan ne don nuna wa gwamnatin cewa a shirye suke su tattauna da ita don sako sauka ‘yan matan da suke hannunsu.

You may also like