BOKO HARAM Osinbajo Ya Umarci Shugabannin Soji Su Koma Jihar Barno


Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya umurci shugabannin hafsoshin sojin Najeriya da su koma jihar Borno domin magance hare-haren Boko Haram da yayi sanadiyyar mutuwar ma’aikatan kamfanin matatar mai a kasa NNPC da suke nemo mai a yankin Chadi.

Ya fadi haka ne bayan tattaunawar da yayi da shugabannin rundunar sojin a fadar gwamnati.

Ministan mai Ibe Kachikwu ne ya sanar wa manema labarai haka bayan ganawa da su da mukaddashin shugaban kasa yayi.

Gidan jaridar PREMIUM TIMESt a rahoto cewa Boko haram ta kashe kuma ta sace wasu ma’aikatan hako danyen mai a yankin Chadi tare da wasu jami’an tsaron da ke tsare da su da wasu malaman jami’ar Maiduguri wanda biyar daga cikin su suka rasa rayukan su.

Bayan hakan ministan tsaro Mansur Dan-Ali ya ce tura shugabanin sojin zai taimaka wajen ganin an kara dakile aiyukkan Boko Haram kamar yadda aka samu a baya.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin za ta samar da na’urorin hangen nesa da wanda zai samar wa sojoji bayanan sirri domin tunkarar Boko Haram din kafin su kai musu hari kamar yadda suke yi a dan kwanakinnan.

You may also like