Boko Haram Sun Kai Sabon Hari Adamawa 


Yan tada kayar bayan Boko Haram sunyi garkuwa da mutane jiya

Wannan ya faru ne bayan sun saki bidiyon da ke nuna yan matan Chibok

Mutane da dama sun hallaka, an yi garkuwa da wasu a sabuwar harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai ungiwar Pallam da ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa.

Rahoto ya nuna cewa sai aka kwashe sa’o’i biyar yan ta’addan na aika-aika.

Wannan hari ya zo ya faru kimanin mako daya kenan bayan yan ta’addan sun kai irinsa a unguwannin Wanu, Kamale, da kafin Hausa a Michika da Madagali.

Pallam garin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Emmanuel Tsamdu. ne.

Wani mazaunin garin, Abamu Japhet yace: ” Sun silalo garin Pallam misalin karfe 11 na dare kawai suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare 

“Da kyar na samu na gudu wajen buya kafin na tsira; babu wani sojan da ya kawo mana agaji. A yanzu dai bamu san yawan mutanen da aka kashe ba amma abun ba dadi.”

Tabbatar da wannan harin, wani dan majalisan wakilan da ke wakilta Madagali da Michika, Adamu Kamale, yace yan ta’addan sun hallaka dabbobi, sun yi fashi, da kona gidaje

You may also like