Boko Haram sun Kara sace ‘yan mata a Borno. 


 

Rahotanni daga jihar Borno a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, na nuni da cewa wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun hallaka mutane 10 tare da sace mata da kanan yara. 

Wannan lamarin dai ya afku ne yayin wani hari da suka kai a kauyen Kuburubu da ke karamar hukumar Damboa. Tun da daren Asabar 20 ga wannan wata na Agusta da muke ciki ne dai wadannan ‘yan bindigar suka afkawa kauyen na Kuburubu a kan babura, inda suka bude wuta a kan mai uwa da wabi wanda hakan ya janyo nan take suka hallaka mutane 10 wasu da dama kuma suka jikkata kana da dama suka fantsama cikin daji don tsira da rai. 

Mazauna garin sun ruwaito cewa baya ga matasa da mata da yara da suka yi awon gaba dasu yayin harin, mayakan sun kuma kwashi kayan abinci da dabbobi. Kauyen Kuburbu dai ya na tsakanin garuruwan Damboa da Chibok ne inda aka sace ‘yan mata sama da 200 fiye da shekaru biyun da suka gabata. Ya zuwa yanzu dai hukumomi ba suce komai kan wannan hari ba, wanda ke zuwa mako guda bayan da kungiyar ta fitar da faifayen bidiyo da ke nuna ‘yan matan sakandaren garin na Chibok da take garkuwa dasu.

You may also like