Boko Haram sun kashe mutane 3 yayin da aka kashe musu mayaka 2 a jihar Adamawa


Sojoji da mafarauta sun harbe mayakan ƙungiyar  Boko Haram biyu bayan da ya’yan kungiyar suka kai hari kan wani ƙauye dake Madagali.

Mazauna yankin sun ce yan ta’addar dauke da makamai sun dirarwa ƙauyen Pallam  da daren ranar Litinin inda suka shiga dibar kayayyaki da kuma lalata gine-gine.

Wani da ya tsere daga gidan sa, Adiel Yakubu, yace yan ta’addar sun kashe mutane uku tare da raunata wasu da dama kafin daga bisani su cinnawa asibitin garin wuta.

“Mun ji ƙarar bindigogi da kuma hargitsi da  daddare ta haka muka gane cewa an kawo hari. Mun gudu zuwa daji inda muka buya.” ya fadi haka.

Shugaban ƙaramar Hukumar Madagali, Muhammad Yusuf yace maharan sun kashe mai gadi a asibitin ƙauyen, wani mai kanti da kuma wani daban ayayin  harin da ya ɗauki tsawon sa’a guda.
Yankin Madagali ya fuskanci hare-hare da dama tun bayan da aka kwato yankin daga hannun kungiyar Boko Haram a shekarar 2015.

You may also like