Alhaji Yusuf Muhammad, shugaban ƙaramar hukumar Madagali ya tabbatar da mutuwar mutane biyar a ƙauyen Kaya a wani hari da ake zargin kungiyar Boko Haram da kaiwa.
Da yake magana da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, Muhammad ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 10:30 na dare.
Ya ce mutane da dama sun samu raunuka ya yin da aka lalata gidaje da kuma sauran kayayyaki ya yin kai harin.
Ya ce sakamakon yawan hare-hare da ake kaiwa kan garuruwa da kuma ƙauyuka dake yankin, mutane na barin yankin zuwa wasu yankuna na jihar da kuma ƙasar Kamaru mai makwabtaka da yankin.
“Mutane biyar aka kashe a wani harin dare da aka kai kan ƙauyen Kaya dake kusa da garin Gulak.
“Kwanaki uku da suka wuce an kashe wasu mutane uku a ƙauyen Pallam, Muhammad ya ce.
Ya ce daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa yanzu yankin ya fuskanci hare-hare masu munin gaske har guda tara.
Mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar Adamawa, Othman Abubakar ya tabbatar da faruwar kai harin.
Abubakar ya ce har yanzu rundunar na tattara bayanai kan harin.